1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin Wasanni: Gasar kwallon kafar Turai

Mouhamadou Awal Balarabe RGB
October 25, 2021

An yi ruwan kwallaye a wasannin kece raini da suka gabata a wasu manyan lig-lig na kasashen Turai ciki har da Holland da ingila inda Liverpool ta kwance wa Manchester united mazagi a kasuwa.

https://p.dw.com/p/429t3
UK Premierleague | Manchester United vs Liverpool
Mohamed Salah na Manchester UnitedHoto: Oli Scarff/AFP/Getty Images

An yi ruwan kwallaye a wasannin kece raini da suka gabata a wasu manyan lig-lig na kasashen Turai ciki har da Holland da ingila inda Liverpool ta kwance wa Manchester united mazagi a kasuwa. An yi abin fallasa a wasannin neman kai wa matakin rukuni na gasar zakarun kasashen Afirka, inda TP mazambe ta Kwango da ASEC Momasa ta Abidjan suka kasa kai labari

An fara daukar matakin cusa wa matasa wasan damben gargajiya a zukuta a jamhuriyar Nijar, baya ga wasan kokawa da ya yi shuhura a wannan kasa ta yammacin Afirka. Za mu yaye kallabin shirin ne da nahiyar Turai, inda aka gwada kwanji tsakanin manyan kungioyyin na lig dabam-dabam na kasashen wannan nahiyar, sai dai a Premier ta Ingila Manchester United ba ta ji da dadi ba a hannun Liverpool.

Liverpool ta kunyatar da Manchester United a filin kwallon Old Trafford da take ji da shi inda ta zazzaga mata kwallon 5-0 a jiya Lahadi ba tare da ta rama ko da daya ba. Wannan ne karon farko da Liverpool ta yi irin wannan kece wa Manchester United mazagi a kasuwa a Old Trafford. Amma Liverpool ta taba doke Manchester United da 7-1 amma a Anfield a shekarar 1895. Kuma wannan shi ne karon farko cikin shekaru 85 da dan wasa daya ya zira wa manchester kwallaye uku a cikin shekaru 85 da suka gabata. Godiya ta tabbata ga dan kasar Masar Mohamed Salah, wanda ya ci uku daga cikin kwallayen, kuma ya tauye taurarin Cristiano Ronaldo na kasar Portugal. A yanzu dai, salah ya zama gwarzon dan kwallon Afrika da ya fi cin kwallo a tarhin Premier lig, inda yake da kwallaye 107, yayin da dan wasan gaba dan Ivory Cote d' Ivoire Didier Drogba ke biya masa baya da kwallaye 104.

A la Lig don kasar Holland da la Liga na kasar Spain ma duk kanwar ja ce, inda aka jijjiga kungiyoyin da ake ji da su. Ajax Amsterdam ta wulakanta PSV Eindhoven inda  ta doke su da ci 5-0 a karawar mako na goma. Dama dai su manyan kungiyoyin na kasar Holland ne suke saman teburin lig da aka fi sani da suna Eredivisie. A yanzu dai Ajax tana saman teburi kuma akwai tazarar maki hudu tsakaninta wacce ke a matsayi na biyu.

Spanien LaLiga | Barcelona vs Madrid
Madrid ta ci Barcelona 2-1Hoto: Josep Lago/AFP

A la Liga kuwa, Real Madrid ta samu nasara da ci 2-1 a kan abokiyar adawarta Barcelona kuma a gida Barcelona ​​a wasan mako na 10 na gasar La Liga . A La Liga inda Barcelonans ke baya a matsayi yayin da Madrid ke kan gaba. Wannan wasa da ke zama na 247 tsakanin kungioyyin biyu ya haifar wa Barcelona da rauni a teburin lig din.

A Faransa kuwa, an yi kare jini, biri jini tsakanin Olympik de Marseille da paris Saint Germain, ba tare da wata daga cikinsu ta samu nasara ba, inda aka tashi wasan neman da nema. Hasali ma alkalin wasa ya soke kwallo da Paris da kuma kwallon da Marseille suka ci bayan da bidiyo ya tantance abin d ya faru.

Yanzu kuma sai mu zo nan gida Jamus, inda aka buga wasannin mako na Bundesliga, kuma kamar yadda aka saba Bayern Munich ta sake samun nasara. A wannan karon dai Hoffenheim ce ta dandana kudarta a hannun Bayern Munich da ci 4-0 a filin wasa na Allianz Arena, musamman sakamakon kwallonsa na goma da Robert Lewandowski ya ci a bana. Shi dai dodon raga dan asalin kasar Poland, wanda ke daya daga cikin wadanda aka sa ran za su iya lashe kyautar Ballon d'Or, ya bayyana cewa yana yin iya kokarinsa don lashe wannan bajinta.

Har yanzu Bayern Munich ce ke kan gaba a teburin Bundesliga, inda ta yi wa Borussia Dortmund ratar maki biyu. Ita dai Dortmund da ta sha duka tamkar kurar roko a hannu Ajax amsterdam da ci 4-0 a gasar zakarun Turai, ta huce haushinta a Bielefeld da ci 3-1, duk da rashin bugawa daga Erling Haaland. Ita kuwa Freiburg tana a matsayi na uku, bayan da ta doke Wolfsburg da 2-0, lamarin da ya yi sanadiyar korar Mark van Bommel, mai horas da Wolfsburg, wanda ya baras da wasanni takwas tun bayan fara kaka. A sauran wasannin na bundesliga fa, musmaman wasan da aka yi tsakanin makwabta biyu Köln da leverkusen?

Bundesliga | RB Leipzig v SpVgg Greuther Fürth
Leipzig ta lallasa Fürth da ci 4-1Hoto: Cathrin Mueller/Getty Images

A sauran wasannin kuma, RB Leipzig ta sami nasara a kan Greuther Fürth 4-1. Da irin wannan sakamakon ne ita Mainz ta doke Augsburg. ita kuwa Hertha Berlin ta yi wa monchengladbach ci 1-0, Union Berlin ta yi kunnen doki 1-1 a Stuttgart, kuma a karshe VfL Bochum ta samu nasarar ta biyu a kakar bana inda ta doke Eintracht Frankfurt da ci 2-0. A jimlance dai, Kwallaye 29 aka zira a mako na tara na Bundesliga. 


A nahiyar Afirka kuwa, zagaye na biyu na wasannin neman hayewa matakin rukuni na gasar cin kofin zakarun nahiyar ya gudana a karshen mako, Kuma an sami sakamakon ban mamaki a wasu wasannin, TP Mazembe ta Kwango Dimukaradaiyya da ta lashe gasar zakarun Afirka sau biyar a tarihinta ba za ta buga wasan rukuni a bana ba, saboda a wasanta a gida Lubumbashi ta yi kunnen doki 1-1 da Amazulu ta Afirka ta Kudu. Wannan yana nufin cewa fitar da TP saboda rashin kwallayen da ta zira a waje a zagayen farko. Wannan dai shi ne karon farko a tarihin kungiyar Amazulu ta Durban, wanda shahararren dan wasan gaba Benni McCarthy ke horarwa ta shiga matakin gasar zakaru.

Har ila yau, ruwa ya kare wa ASEC Mimosas ta Abidjan wacce rashin nasara da ta yi da ci 0-2 a hannun CR Belouizdad ta Algiers ya sa aka yi waje road da ita sakamakon rashin kare ci 3-1 da ta yi a makon da ya gabata. Amma kuma a gefe guda, ta ware wa giwayen kwallon kafar Afirka da suka fito daga kasashen Larabawa wato Al Ahly ta Masar da Zamalek, sai kuma kungiyoyin biyu na Casablancan don Moroko (Raja da Wydad) da kuma Esperance de Tunis da Etoile du Sahel. Ita ma Horoya ta Guines ta cancanci hayewa matakin rukuni bayan da ta samu nasara a fafatawa da ta yi da Stade Malien da ci 2-1. Za a hada jadawalin matakin rukuni na gasar zakarun Afirka ne walau a watan Disamba ko kuma Janairu mai zuwa. 

A jamhuriyar Nijar, kasar da kokawa ke zama wasan da aka fi ji da shi a fadin kasar, inda a kowace shekara ake shirya gasar cin takobi. Sai dai sannu a hankali, masu sha'awar damben gargajiya ta kasar Hausa, sun fara bai wa matasa kwarin gwiwar shiga wasanin a nan gaba.