1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin Labarin Wasanni

Suleiman Babayo LMJ
September 28, 2020

Ina aka kwana kan wasannin lig na Jamus wato Bundesliga? Za mu ji halin da ake ciki game da fara komawa wasannin a Jamhuriyar Nijar bayan annobar cutar coronavirus.

https://p.dw.com/p/3j6dJ
Fußball Bundesliga TSG Hoffenheim - FC Bayern München
TSG Hoffenheim ta bai wa Bayern Munich mamaki a karshen makoHoto: Marvin Ibo Güngör/GES/picture-alliance

An kare wasannin mako na biyu a gasar Bundesliga ta Jamus, inda kungiyar Frankfurt ta bi Hertha Berlin har gida ta lallasa ta da ci uku da daya, haka ita ma Stuttgart ta bi Mainz har gida ta doke ta da ci hudu da daya, kuma duka kungiyoyin sun samu jan kati na korar dan wasa daga fili. Kana Augsburg ta samu nasara a kan Dortmund da ci biyu da nema, kungiyar Arminia ta doke FC Cologne da ci daya mai ban hausi, yayin da Werder Bremen ta bi Schalke har gida ta doke ta da ci uku da daya.

Hoffenheim ta samu galaba a kan Bayern Munich da ci hudu da daya, sannan Freiburg da Wolfsburg sun tashi kunnen doki daya da daya kuma haka labarin yake tsakanin kungiyoyin Mönchengladbad da Union Berlin wato suma canjaras da ci daya da daya. Haka kuma an tashi wasa kunnen doki ci daya da daya tsakanin kungiyoyin Leverkusen da Leipzig, wanda kuma shi ne sashen Hausa na DW ya kawo muku kai tsaye. Yanzu haka dai kungiyar Hoffenheim ce ke kan gaba a teburin na Bundesliga da maki shida yayin da Augsburg ke matsayi na biyu ita ma da maki shida. Frankfurt da Leipzig da kuma Frieburg na matsayin na uku da na hudu da na biyar da maki hudu ko waccensu.

England Fußball Manchester United vs. Leicester City
Manchester City ta sha kashi a hannun Leicester City a karshen makoHoto: Reuters/D. Staples

A wasannin Premier League na kasar Ingila kuwa an yi ruwan kwallaye a raga a karshen mako, inda Leicester ta doke Manchester City da ci biyar da biyu, West Harm ta lallasa Wolverhamton da ci hudu da nema, kana Manchetser United ta samu nasara kan Brigton da ci uku da biyu. A La Ligar kasar Spain kuwa kungiyar Atlético Madrid ta yi cin kacar tsohon keke rakacau a kan kungiyar Granada da ci shida da daya yayin da Barcelona ta samu galaba kan Villarreal da ci hudu da nema.

A karon farko a tsawon tarihi kasar Saudiyya za ta karbi bakuncin wasannin kwararru na kwallon lambu wato Gulf na mata na duniya, a watan Nuwambar wannan shekara. Za a kara wasannin a filayen wasan kwallon lambu guda biyu da ke birnin Jeddah na kasar ta Saudiyya tsakanin 12 da 15 ga watan na Numwamba. A Jamhuriyar Nijar kuwa hukumomin wasannin motsa jiki dabam-dabam na kasar, sun soma shirye-shiryen kammala wasannin shekarar bana, ko kuma na shiga sabuwar kakar wasannin shekarar badi, bayan da gwamnatin kasar ta ba da izinin bude filayen wasannin da aka rufe tsawon watanni shida a sakamakon annobar COVID-19.