1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin Labarin Wasanni

Mouhamadou Awal Balarabe LMJ
January 25, 2021

Tafiya ta fara nisa a gasar kwallon hannu ta duniya da a yanzu haka, take gudana a kasar Masar. Za mu leka Bundesligar kasar Jamus mu ji wainar da ake toyawa.

https://p.dw.com/p/3oOcO
Handball WM Schweden - Ägypten
Hoto: Xinhua/picture alliance

Kasar Masar ta tsallake zuwa matakin kusa da kusa da na karshe biyo bayan kunnen doki da ta yi 25-25 da Sulobeniya, kasar da 'yan wasanta da dama suka kamu da kwayar cutar corona. Hasali ma Masar ce kawai za ta ci gaba da wakiltar Afirka a wannan matakin gasar, saboda an yi waje da sauran kasashen da ke wakiltar wannan nayiha. Sai dai kungiyar kwallon hannu ta Masar na da jan aiki a gabanta a ranar Laraba mai zuwa a birnin Alkahira, saboda za ta hadu ne da kasar Denmark da ke zama zakaran wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya. Sau hudu ne dai Masar ta taba kai wa matakin daf da na kusa da na karshe wato 'quater final' a gasar duniya hudu a jere, har ma ta taba kai wa ga wasan kusa da na karshe a shekarar 2001 da Faransa.

Fußball Afrikanische Nationenmeisterschaft 2021 Marokko - Togo
Fafatawa tsakanin kasashen Moroko da Togo, a gasar cin kofin kwallon kafa na 'yan wasan da ke buga kwallo a gidaHoto: Alain Guy Suffo/Sports Inc/empics/picture alliance

A nahiyar Afirka kuwa, gasar neman cin kofin kwallon kafa na 'yan wasan wannan nahiya da ke bugawa a kasashensu na asali, ta shiga rana ta uku kuma ta karshe a matakin rukuni. Tuni ma dai kasar Kamaru da ke karbar bakuncin gasar, ta tsallake zuwa zagayendaf da na kusa da na karshe wato 'quater final', bayan da ta tashi canjaras babu ci tsakaninta da Burkina Faso. Wannan ya bai wa Indomitable Lions damar zuwa zagaye na biyu a rukuninsu na farko, yayin da Mali wacce ta lallasa Zimbabuwe da ci daya mai ban haushi, ta zama ta daya, inda Zimbabuwe da Burkina Faso suka tattara komatsansu sun koma gida.
Wasanni biyu na karshe na rukuni na biyu za su gudana ne tsakanin Kwango-Brazzaville da Libiya, yayin da Mena ta Jamhuriyar Nijar za ta fafata da Jamhuriyar Dimukaradiyar Kwango. Sai dai wannan rukuni ya zama na kowa ta sa ta fisshe shi, saboda sai an kammala wasanni ne za a iya samun haske dangane da wadanda suka cancanci zuwa zagaye na gaba.  Sai dai 'yan Nijar da dama na nuna damuwa dangane da yadda 'yan wasan kasarsu suka gaza taka rawar gani a wannan gasa, duk da cewa sun bayar da mamaki a wasannin sada zumunta na share fagen zuwa wannan gasa. 

A nan Tarayyar Jamus, bayan nasarar da ta samu a wasannin mako na 18 a karshen mako, Bayern Munich ta karfafa matsayinta a saman teburin Bundesliga bayan da ta doke  Schalke 04 da ci hudu da nema. Wannan nasarar ta sanya kungiyar yi wa mai biya mata baya ratar maki bakwai, lamarin da ya kasance abin farin ciki ga mai horsa da 'yan wasan kungiyar ta Bayern Hansi Flick: "Ina ganin cewa za mu iya yin abubuwa da yawa kuma dole ne mu yi su da kyau. Dole mu yi nazarin kowane wasa, mu aiwatar da salon kwallon kafa da muka tsara. Ba shakka, idan zai yiwu, mu gudanar da wasa mai ban sha'awa."

Bayern Munich ta sami wannan ci gaba ne saboda manyan abokan hamayyarta ba su kai labari ba a karshen mako. Kungiyar RB Leipzig ta Julian Nagelsmann ta dibi kashinta a hannun kurar baya Mainz wacce ta doke ta da ci uku da biyu. Wannan koma-baya zai iya dakushe fatan Leipzig na zama zakara, kamar yadda dan wasanta na tsakiya Marcel Sabitzer ya bayyana. Ita kuwa Bayer Leverkusen ta Peter Bosz Wolfsburg ce ta bi ta har gida kuma ta doke ta da ci  daya mai ban haushi.
A nata bangaren, Borussia Dortmund ta gudanar da wasa na uku a jere ba tare da samun nasara ba, inda takwarta Borussia Mönchengladbach ta lallasa ta da ci hudu da biyu. A yanzu Dortmund na matsayi na bakwai a teburin Bundesliga. A cewar Marco Reus kyaftin din kungiyar, komabayansu ba ya rasa nasaba da kurakuran da suke yawan tafkawa a baya: "A yanzu haka muna shan bugu da yawa, kuma dole ne mu hakura da shi. Muna sanya karfi sosai don fance kwallon da ake bin mu, kuma kwalliya ba ta biyan kudin sabulu: Yana bukatar kuzari sosai, amma ba ma shan romonsa duk da kokarin da muke yi. Ya kamata mu zura kwallo tun kafin mu tafi hutun rabin lokaci. Kuma ko da yake rabin lokaci na biyu bai kai zafin na farko ba, amma sam sam bai kamata a zura mana kwallo kamar na uku ba."

Deutschland Bundesliga Borussia Mönchengladbach vs Borussia Dortmund
Ba sa'a ga Borussia Dortmund a kakar Bundesliga ta banaHoto: Martin Meissner/AP Photo/picture alliance

A yanzu dai Borussia Mönchengladbach ta koma matsayi na biyar, yayin da Eintracht Frankfurt ke a matsayi na shida kuma na karshe zuwa gasannin Turai, bayan da ta samu nasara a kan Arminia Bielefeld da ci biyar da daya. A sauran wasanni kuwa, Hertha Berlin da ta yi wasa a gida ta sha kashi da ci hudu da daya a hannnun Werder Bremen da ke a matsayi na 14. Kuma bayan wannan koma-baya, Hertha ta kori daraktan wasanninta Michael Preetz da mai horas da 'yan wasanta Bruno Labbadia. Ita kuwa Hoffenheim ta yi wa Cologne dukan kawo wuka da ci biyar da nema. Ita ma Augsburg ta doke Union Berlin da ci biyu da daya, haka kuma bin yake a wasan tsakanin Freiburg da ta samu nasara a kan Stuttgart da ci biyu da daya.

Japan Tokio | Werbung Olympische Sommerspiele 2020
A bara annobar coronavirus ta tilasata dage gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle da za a yi a birnin TokyoHoto: Behrouz Mehri/AFP/Getty Images

Gwamnatin Japan ta jaddada aniyarta ta shirya gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle wato Olympic ta Tokyo a lokacin bazarar wannan shekarar, duk da jita-jitar da ake yadawa cewa tana kasa a gwiwa sakamakon yaduwar annobar corona. A lokacin da yake bayani a zauren majalisar dokokin kasarsa, Firaminista Yoshihide Suga ya kuduri aniyar shirya gasar lami-lafiya domin nuna nasarar da dan Adam ya samu a kan kwayar cutar coronavirus.

Shi ma kwamitin shirya wasannin na guje-guje da tsalle-tsalle, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa yana mai da hankali sosai kan shirye-shiryen karbar bakuncin wasannin na Olympics, bisa goyon bayan gwamnatin Japan da kuma  Kwamitin Shirya Gasar Olympic na Duniya. A shekarar da ta gabata ne da ya kamata a gudanar da wasanni a birnin Tokyo, amma aka dage su sakamakon barkewar annobar corona da duniya ke fuskanta. Wata kididdigar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar, ta nuna cewa akasarin 'yan Japan na fatan ganin an dage wasannin na guje-guje da tsalle-tsalle zuwa wani lokaci.