1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Labarin Wasanni 01.11.2021

Suleiman Babayo MA
November 1, 2021

Daga ciki muna dauke da cin kacar tsohon keke da Bayern Munich ta yi wa Union Berlin a gida, inda ta yi mata 5-2.

https://p.dw.com/p/42RBj

Farko za a ji bayanai a kan wasannin Bundesliga na Jamus da ake karawa da sakamakon da suka samu kawo yanzu. A wasannin lig na Ingila da ake kira Premier, kungiyar Manchester United ta yi tattaki har gida ta doke Tottenham 3 da nema.

Bayan da mazauna birnin Sydney da kewaye a jiha mafi girma na Australiya wato New South Wales suka shafe kwanaki 100 suna zaune a gida sakamakon dokar corona, mahukuntan jihar sun amince al’ummomin da abin ya shafa su fara fita yin wasannin motsa jiki.

Shahararren dan wasan tennis na duniya, Novak Djokovic, ya ce burinsa shi ne ci gaba da jan zare a matsayi na farko a tsakanin gwanayen har zuwa karshen wannan shekara ta 2021.