1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Firaministan Girka cikin tsaka mai wuya

Abdourahamane Hassane
November 7, 2022

Firaministan Girka Kyriakos Mitsotakis na fuskantar matsin lamba daga 'yan adawa, wadanda ke neman karin haske game da badakalar satar sauraran bayyanan wayoyin wasu manyan jami'an gwamnati ba bisa ka'ida ba.

https://p.dw.com/p/4JAik
Kyriakos Mitsotakis firaministan Girka
Kyriakos Mitsotakis firaministan GirkaHoto: Thanassis Stavrakis/AP Photo/picture alliance

Jam'iyyar masu tsattsauran ra'ayi ta tsohon firaministan Alexis Tsipras  Syriza, ta bukaci a ba da haske kan wannan al'amari kafin zabuka masu zuwa da aka shirya yi a lokacin rani na shekara ta  2023. Jam'iyyar ta adawa ta Girkan ta ce tana tunanin yin amfani da kuri'ar yankan kauna a majalisar dokoki don adawa da gwamnatin Conservative, wadda ke da rinjaye a majalisar. Daga cikin wdanda ake zargin hukumar leken asirin Girkan ta rika satar sauraran bayyanan wayoyinsu na hanu har da tsohon firaministan kasar Antonis Samaras da wasu 'yan jaridar na adawa da kuma wasu ministocin.