1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kyautar Nobel ta shekara ta 2011

October 6, 2011

An bada kyautar ta rubuce rubuce ta wannan shekara ga wani ɗan ƙasar Sweden Tomas Tranströmer,

https://p.dw.com/p/12n8I
Tomas TranstromerHoto: dapd

An bada kyautar Nobel ta rubuce rubuce ta wannan shekara ga wani marubucin waƙe na ƙasar Sweden.Hukumar accdemy ta ƙasar SwEden ta baiyanna Tomas Transtromer mai shekaru 80 a duniya da cewa shi ne ya samu kyataur ta wannan shekara.

Transrtomer wanda ya fara rubuta litatafai na waƙe tun ya na da shekaru 23 da haifuwa wanda yawan su ya zarta guda 17 ;ya na fama da mutuwar rabin jiki bayan wani hatsarin da ya samu a shekara ta 1990.Kawo yanzu dai litatafan da ya rubuta wanda aka fara wallafawa tun a shekarun 1950 an fasara su a cikin harsuna daban daban har guda 60.kyautar dai ta hada da kuɗaɗe tsaba wanda yawansu ya kai sama da miliyion ɗaya na Euro.

Mawallafi:Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar