1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Firaministan Habasha ya mamaye sharhin jaridun Jamus

Zainab Mohammed Abubakar
October 18, 2019

Hankalin jaridun Jamus ya karkata kan batun karrama fraiministan Habasha da aka bai wa lambar yabo ta zaman lafiya, da zaben kasar Mozambik da sai kuma matsalar siyasa a yaki da yaduwar cutar Ebola a Kwango.

https://p.dw.com/p/3RXCM
Friedensnobelpreis 2019 Äthiopien | Ministerpräsident Abiy Ahmed
Firamnistan Habasha Abiy AhmedHoto: Ethiopian Prime Minister Office

Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta wallafa mai taken " Abiy Ahmed ya samu lambar yabo ta Nobel kan zaman lafiya, biyo bayan warware rikicin kan iyaka da Eritrea". Jaridar ta cigaba da cewar kwamitin da ke da alhakin bada lambar yabon kan zaman lafiya, ta zabi fraministan mai shekaru 43 da haihuwa a matsayin wanda ya lashe lambar yabon ta Alfred Nobel na wannan shekara ta 2019.

A birnin Oslo na kasar Norway, kakakin kwamitin Berit Reiss-Andersen ta ce, kwamitin ya karrama kokarin Abiy  saboda hobbasarsa kan tabbatar da zaman lafiya da hadaka na kasa da kasa. Inda ya cimma nasarar warware takaddamar da ke tsakanin Habasha da makwabciyarta watao Iritiriya.

A hirar ta da maneman labarai, Reiss-Andersen ta kara da cewayar ko shakka babu hannu daya baya daukar jinka, idan ana maganar cimma sulhu kan rikicin kan iyaka, wajibi ne sai daya bangaren ma ya amince kafina cimma sulhu. Sai dai fraiministan Habasha Abiy Ahmed ne kadai ya samu wannan karramawa. Sai dai babu masaniya dangane da ko za a gayyaci takwansa na Iritiriya a ranar 10 ga watan Disamba da za a bada  lambar yabona birnin Oslo.

Zaben kasar Mozambik ya ja hankalin a Jaridun JamusA sharhinta na wannan makon jaridar die Tageszeitung sharhinta da ta rubuta game da zaben da aka gudanar a Mozambik, cewa ta yi sakamakon zaben da aka gudanar zai kasance zakaran gwajin dafin yarjejeniyar sulhu mai tangal-tangal da aka cimma tsakanin jam'iyyar da ke mulki ta Frelimo da babbar abokiyar adawarta da suka gwabza fada da ta rikide zuwa adawa watau Renamo.

Wahlen Mosambik
Malaman zabe a kasar MuzambikHoto: DW/C. V. Teixeira

Jaridar ta cigaba da cewar zaben ya kasance wanda aka yi shi a bude a tarihin kasar Mozmabik. Sai dai a a yayin da mutane miliyan 13 da suka yi rijistar kada kuri'unsu suka kama hanyar zuwa rumfuna dubu 20 da aka tanada, akwai fargabar shakku kan sahihancin sakamakon da zai biyo baya. 

Ba wai shugaban kasar ne ke neman Ta-zarce kan mukaminsa a karon farko ba, amma har da 'yan majalisar kasa da ma gwamnonin gundumomi 10 da ke kasar ta Mozambik, bisa ga yarjejeniyar da suka cimma a baya bayannan a watan Agusta da bangaren adawa watau Renamo. Inda hakan ne zai baiwa Renamon damar samun manyan mukamai a cikin gwamnati.

Siyasa ta mamaye yaki da cutar EbolaJaridar Neues Deutschland labari ta buga dangane da yadda tsoma batun yaki da annobar Ebola cikin harkokin siyasa ya haifar da tafiyar hawainiya a yaki da cigaban yaduwar cutar a kasar Janhuriyar Dimukuradiyyar Kwango. 

Demokratische Republik Kongo | Ebola Epidemie
Jami'an kiyon lafiya na lura da Ebola KwangoHoto: Getty Images/AFP/A. Wamenya

A cewar hukumar kula da lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya kokarin da ake yi na dakile karuwar yadauwar cutar na fuskantar tafiyar hawainiya. Inda rikice-rikice da ma yadda lamura ke tafiya a sashin kula da lafiya a kasar ta Kwango na haifar da matsaloli. 

A shekara ta 1976 ne dai annobar ta fara barkewa a yankin arewa maso yammacin kasar ta Kwango, cutar da ke yaduwa tsakanin jama'a ta hanyar zazzabi mai tsanani da gudawa, kuma idan yayi tsanani a fara fitar da jini ta gabobi. 

A tsakanin shekara ta 2014-2016 cutar Ebola ta yadu kasashe da dama da suka hadar da yankin Afirka ta Yamma. tun daga watan Agustan 2018, sama da mutane dubu uku suka kamu, daga cikinsu sama da dubu biyu suka rasa rayukansu.