1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta karrama sojanta da ya mutu a Nijar

Ramatu Garba Baba MNA
August 17, 2019

An karrama La David Johnson da ya mutu a yayin wani harin da mayakan jihadi suka kai kan tawagar rundunar sojin Amirka a jamhuriyar Nijar a shekarar 2017.

https://p.dw.com/p/3O3G0
US Soldat  La David Johnson starb am 4. Oktober 2017
Hoto: imago/Zumapress/Us Army

An mika kyautar girmamawar, mafi girma da ake bai wa duk wani jami'i da ya mutu a fagen daga, ga iyalan mamacin a jihar Florida a yammancin ranar Juma'a. Mayakan jihadi fiye da dari ne suka yi wa Sajan Johnson da rundunar kawanya, a yayin da suke farautar wani jagoran kungiyar IS da ayyukansa suka addabi al'ummar yankin Afirka ta Yamma. Soji hudu ne suka rasa rayukansu a sanadiyyar harin na wancan lokacin.