1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kyanda ta yi kisa a Zimbabuwe

August 17, 2022

Hukumomin kasar sun ce sun tashi haikan wajen ganin sun kara azamar yi wa yara rigakafi, sannan kuma sun amince da fitar da kudade na musamman domin yaki da cutar ta kyanda cikin gaggawa.

https://p.dw.com/p/4FdMb
Simbabwe Präsidentschaftswahl Emmerson Mnangagwa erklärter Wahlsieger
Hoto: Getty Images/D. Kitwood

Cutar kyanda ta kashe akalla kananan yara 157 a kasar Zimbabuwe da yankin Kudanin Afirka. Ministar yada labaran kasar Monica Mutsvangwa wacce ta sanar da haka a ranar Talata ta ce kawo yanzu an samu yara sama da 2,000 da cutar ta kama.

A farkon watan ne dai hukumomi suka sanar da barkewar cutar a kasar, kuma tun daga lokacin cutar da ke saurin kisan kananan yara ke kara yaduwa.

A watan Afrilun da ya gabata Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce cututtukan da a kan iya samun kariya daga gare su na kara yaduwa a Afirka, inda ta nuna damuwa kan yadda cutar ta kyanda ke saurin yaduwa a nahiyar.