1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kyaftin Traoré: "karfin abokan gaba ya karu"

Mouhamadou Awal Balarabe
July 23, 2023

Shugaban gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso Kyaftin Ibrahim Traoré ya amince cewar karfin 'yan ta'adda da ke haddasa tashin hankali a kasar ya karu matuka sakamakon yadda suke sabunta kayan aikinsu.

https://p.dw.com/p/4UHd8
Shugaban gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso Kyaftin Ibrahim TraoréHoto: AA/picture alliance

A wani jawabi da ya yi ga rundunoni na musamman da ke yaki da ayyukan ta'addanci da ke da cibiya a kusa da birnin Ouagadougou, Kyaftin Ibrahim Traoré ya ce masu ikirarin jihadin na sabunta kayan aikinsu domin ya dace da halin da ake ciki. Amma shugaban gwamnatin mulkin sojin ya yi alkawarin kara horas da sojojin Burkina Faso da kuma uwa uba samar da jirage yaki don tinkarar abokan gaba.

Sama da CFA biliyan daya ne dai aka tattara tun daga watan Oktoba (kimanin Euro miliyan 1.5) bayan kiran da hukumomin soji suka yi wa 'yan Burkina Faso na ba da gudummawa ga yunkurin sayan kayan yaki don sake kwato yankunan da ke karkashin kulawar 'yan ta'adda. Tun a shekaru takwas da suka gabata ne Burkina ta fada tarkon kungiyoyin da ke da'awar jihadi masu alaka da kungiyar IS da al-Qa'ida, wadanda suka kashe fararen hula da sojoji sama da 16,000.