1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwashe ma'aikatan Japan daga tashar Fukushima

March 21, 2011

A daidai lokacin da ake haramta wa al'umar da ke rayuwa kusa da Fukushima cin wasu nau'o'in abinci, gwamnati ta fara kwashe ma'aikata daga tashar saboda suna cikin hadari.

https://p.dw.com/p/10dKL
Ma'aikatan Fukushima a lokacin jigilar kayan ofisHoto: AP

An kwashe jami'an da ke aiki a cibiyar makamashin nukiliyar nan ta Fukushima ta Japan, bayan da hayaki ya fara fitowa daga sundukan nukiliya guda biyu wadanda su ka fi lalacewa sakamakon girgizar kasa. Wannan dai ya zo ne kwana guda bayan da firaminista Naoto Kan ya bayyana cewar an fara shawon kan matsalar lalacewar cibiyar sannu akan hankali.

Sai dai fa ma'aikatar lafiya ta Japan ta yi kira ga mazauna unguwannin da ke kusa da cibiyar nukiliyar ta Fukushima, da su kaurace wa shan ruwan pampo, bayan da aka gano wasu sinadarai masu guba da ka iya illata bil adama. Kazalika ma'aikatar ta haramta sayar da madara daga wani kamfani a garin na Fukushima, da ma dai alayyahu da ake nomawa a yankin.

Kungiyar lafiya ta duniya ta bayyana cewa illar tururin da aka samu a kayan abinci a yanzu ta fi yadda aka zata, duk da cewa kawo wannan lokacin ba a samu rahoton wani gurbataccen abinci ya isa wata kasa ba. A yau litinin ne firaminista Naoto Kan yayi niyar ziyartar wuraren da girgizar kasar ta fi kamari a jirgi mai saukar ungulu. Sai an soke ziyarar saboda ruwa da ake tafkawa kamar da bakin kwarya.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar