1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kwango ta ce Ruwanda ta kai mata hari

June 11, 2022

Rundunar sojin Kwango ce ta sanar da wannan zargi, inda ta ce a ranar Jumma'a, da tsakar rana, Ruwanda ta kai harin a arewacin lardin Kivu da ke gabashin Kwango mai fama da fitintinu.

https://p.dw.com/p/4CYqF
Kombibild Felix Tshisekedi und Paul Kagame

Gwamnatin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ta zargi Ruwanda da kashe mata dalibai guda biyu a yayin wani hari da Ruwandan ta kai a wata makaranta da ke cikin kasar Kwango.

Hukumomin Kwango sun ce munin abin da Ruwanda ta aikata daidai yake da laifukan yaki. Sai dai wannan na zuwa ne 'yan sa'o'i bayan da Ruwanda ta zargi Kwango da harbo makaman roka cikin kasar ta. 

Zaman doya da manja na kara ruruwa a tsakanin kasashen makwabtan juna a sakamakon zargin juna da suke yi na tallafa wa 'yan tawayen da ke ci gaba da halaka mutane a kan iyakar kasashen.