SADC ta bukaci a sake kidayar kuri'u a zaben Kwango
January 13, 2019Talla
SADC din ta mika wannan bukata ce ga Kwango a wannan Lahadin, inda ta ke cewar sake yin kidayar zai taimaka wajen kwantar da hankalin wadanda su ka yi nasara da wadanda su ka sha kaye a zaben na wata Disamabar shekarar da ta gabata.
A share guda kuma kungiyar ta bukaci 'yan sayasar kasar da su yi dukannin mai yiwuwa wajen ganin sun girka gwamnatin hadin kan kasa wadda za ta bada dama a yi tafiya da dukannin bangarori na siyasar kasar don a samu zaman lafiya mai dorewa.
Wannan bukata da SADC ta gabatar na zuwa ne bayan Martin Fayulu wanda ya zo na biyu a zaben na Kwango ya bukaci kotun kolin kasar da ta soke zaben baki dayansa saboda zargin tafka magudi.