Mahukunta a yankin Arewa maso Yammacin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, sun sanar da gano gawarwakin mutane 28 a kogin kasar yayin da wasu da dama suka yi batan dabo biyo bayan kifewar wani kwale-kwale.
https://p.dw.com/p/4XYtK
Talla
Mahukuntan na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, sun sanar da cewa kwale-kwalen ya tashi ne daga garin Mbandaka zuwa yankin Bolomba da ke Arewa maso Yammacin Kwangon, kafin ya kife ya kuma nutse cikin dare a ranar Jumma'ar da ta gabata.