1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwango: Har yanzu da sauran rina a kaba

Abdoulaye Mamane Amadou
May 6, 2019

Felix Tshisekedi ya cika kwanaki 100 kan madafan iko to amma sai dai har yanzu shugaban ya kasa samar da firaminista da zai tafiyar da aiyukan gwamnatin kasar

https://p.dw.com/p/3I02R
Präsident des Kongos: Felix Tshisekedi
Hoto: Getty Images/AFP/S. Maina

Kwanaki 100 na karbar rantsuwar Shugaba Felix Tshisekedin dai na zuwa ne a daidai lokacin da daukacin hankullan yan kasar suka koma kansa duba da tarin kalubalai da kasar ta ke fuskanta wanda sabon shugaban Tshikesedi Tchilombo da kansa ya sha aiwarta korafe-korafe a kansu ga gwamnatin Joshep Kabila da ya gada kan madafan iko.

Dalilan da suka sa Felix Tshisekedi da darewarsa kan mulki, ya ambaci daukar matakai na kawo muhimman sauye-sauye da suka shafi tsaro, yaki da cin hanci da tabbatar da walwala da fadar albarkacin baki, da zummar tabbatar da kawo canjin hannu a mulkin kasar.

Sai dai kwanaki 100 har yanzu da akwai sauran rina a kaba in ji Pieter Jan Hamels jagoran wasu kungiyoyin fararen hula masu fafatukar bunkasa kasashen yankin tsakiyar Afirka.

"Shugaban ya yi yunkurin kawo wasu sauye-sauye da ake iya gani a zahiri kamar dakatar wasu masu muhimman mukamai na tsohuwar gwamnatin Kabila, sa'anan kuma ya bukaci fannin shari'ar kasar ya zartar da aikinsa a cikin adalci to amma kuma idan ka lura duk wadannan bukatocin za su yi wuya idan har aka dubi matsalolin da ke zagaye da jagorancinsa duba da rashin gwamnati ga kuma rashin rinjaye a majalisar dokoki kana kuma babu wata yarjejeniya ta siyasa tsakanisa da bangaren masu rinjaye saboda hakan akwai wuya wai gurguwa da auren nesa."

Shugaban Kwango Felix Tshisekedi
Shugaban Kwango Felix Tshisekedi Hoto: Getty Images/AFP/J. Wessels

Masu fafutikar bunkasar kasashen na yankin tsakiyar Afirkan dai sun yi ittifakin cewa, kasar Kwango ba za ji wani sauyin da Tshisekedi yake ambatawa ba, face sai an kawo gyaran fuska ga tsarin kotunan kasar da saka haske da adalci ga batun hako ma'adanun karkashin kasa da Allah ya albarkanci kasar ta Kwango da su.

To amma sai dai wani hanzarin ba gudu ba a tsawon kwanaki 100 kawai na mulki, adadin kasafin kudin da aka kashe a fadar shugaban kasar ya zarta kima da kashi 120 ciki 100 abinda kuma yake bayyane a zahiri da cewar akwai jan aiki a gaba a cewar Pieter Jan Hamels.

"Kowa yana gani a zahiri da cewar kasafin kudin da aka ware ga fadar shugaban kasar sun kashe kudin fiye da kima, domin an lura da cewa kusan kashi 35 cikin 100 na kasafin kudi an sanya su ne a cikin wasu bukatu na musamman alhali kuwa wadannan bukatun na musamman na fadar shugaban kasa ba a tanade su ba a cikin kasafin kenan akwai babban gibi na rashin adalci da rashin lura da yadda ake kashe kudademusamman ma ga wanda ya ce zai yin fito na fito da cin hanci da rashuwa."

Tsohon shugabam Kwango Joseph Kabila
Tsohon shugabam Kwango Joseph Kabila Hoto: picture-alliance/AP/J. Delay

Ko baya ga duk wadannan matsaloli babban abin da ya fi jan hankali shi ne har yanzu shugaba Tshisekedi ya kasa samar da firamisata da zai tafiyar da harkokin gwamnatin kasar alhali kuwa kawancensa na siyasa ya cimma yarjejeniyar zartar da mulki  da kawancen FCC mai marawa tsohon shugaban kasar Joshep Kabila baya.

Sai dai duk da kasawar da ake gani gwamnatin mai kwanaki 100 ta Tshisekedi ta yi wani babban abin tarihin da ya faru a tsawon kwanakinta shi ne na zabar macce ta farko a matsayin shugabar majalisar dokoki. Jeanevive N'agossie wata 'yar majalisar dokoki kasar Kwango ce cewa ta yi:

"Zabar da aka yi an yi ne bisa cancanta ba wai don tana mace ba ce kwararra ce da ta shafe tsawon shekaru fiye da 25 tana aiki."

Tuni dai sabon shugaban ya ki aminta da nada wani na hannun damar tsohon shugaban kan mukamin na firaminista lamarin da ya kara haifar da takaddama ta cikin gida tsakanin kawancen siyasar kasar biyu, a yayin da a share daya kwanakinsa kan kujerar mulki ke dada tsawaita.))