1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana fuskantar matsaloli a yankunan da za a sake zabe

Mouhamadou Awal Balarabe
March 18, 2019

Makonni biyu kafin a gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki, hukumar zaben Kwango ta ce ta na fuskantar kalubale wajen shirya zabe a yankunan da aka dage zabukan bisa aukuwar rikici.

https://p.dw.com/p/3FEm3
DR Kongo Lage nach Wahlsieg von Tshisekedi
Hoto: Reuters/B. Ratner

Mutane 535 ne suka halaka a rikicin kabilanci da ya auku a yankin Yumbi da ke gabashin Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango, lamarin da Majalisar Dinkin Duniya ta danganta shi da cin zarafi mafi muni da aka fuskanta a baya-bayan nan a kasar. Yanzu ma haka kurar rikicin ba ta lafa ba, tashin hankalin ya tilasta wa mutane kimanin dubu 16,000 kaurace wa matsugunansu. A cikin wannan yanayi ne zaben 'yan majalisar dokokin kasa ya kamata ya gudana a ranar 31 ga watan wata na Maris. Saboda haka ne  yawancin jama'ar garin ke nuna damuwa dangane da matsalar tsaro da ake fama da ita.

Amma hukumar zabe mai zaman kanta ta Jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango ta tabbatar da cewa shirye-shiryen gudanar da zaben na 31 ga watan Maris sun yi nisa. Hasala ma, ita CENI ta ce ta tattauna da hukumomin tsaro da na kiwon lafiya don samun hadin kansu wajen tabbatuwar zabe a yankin gabashin kasar, duk da barazanar tsaro da ake fuskanta.

Garin Yumbi na ci gaba da zama fagen faruwar tashin hankali, inda abin da be taka kara ya karya ba, zai iya sake kunna wutar rikicin na kabilanci. John Bosco Lomomo, mataimakin shugaba gamayyar kungiyoyin kare hakkin bil Adama na yankin ya bayyana cewar sanya batun sulhunta kabilun da ke fada da juna tamkar dai riga malam masallaci ne.

Har yanzu, akwai jan aiki a gaban hukumomin Kwango wajen tabbatar da zaman lafiya a Yumbi, duba da aiki na bincike da hukunta masu laifi da ke gabansu. Sai dai a sauran yankuna biyu na Beni da Butumba da zaben zai gudana, al'amura sun fara daidaita bayan harin da aka kai kan cibiyoyin yakin da cutar Ebola da ta haddasa asarar rayukan mutane 587 daga watan Agustan bara i zuwa yanzu.