1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kwango: Jakadu sun bukaci kwantar da hankali

December 24, 2023

Ofisoshin jakadanci na kasashen ketare da ke aiki a Jamhuriyar Dimukuradiyyar kwango, sun bukaci da a kai zuciya nesa dangane da al'amuran da suka biyo bayan zaben shugaban kasar ta Kwango da ke cike da rudani.

https://p.dw.com/p/4aXSb
Hoto: Sarah Meyssonnier/REUTERS

Ofisoshin jakadanci na kasashen ketare da ke aiki a Jamhuriyar Dimukuradiyyar kwangosun bukaci da a kai zuciya nesa dangane da al'amuran da suka biyo bayan zaben shugaban kasar ta Kwango da ke cike da rudani.

Kiran na zuwa ne a daidai lokacin da biyar daga cikin 'yan takara na shugabancin kasar 19, suka sanar da gudanar da zanga-zanga don nuna adawa da sakamakon zaben da hukumar CENI ke fitarwa.

A wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar ofisoshin jakadancin kasashen yammacin duniya 12 tare da ofishin jakadancin Canada da ke birnin Kinsasha, sun bukaci kwantar da hankali, kasancewar han yanzu ana ci gaba da hada sakamakon zaben.

Shugaba mai ci dai  Felix Tshisekedi, na fuskantar hamayya daga 'yan takara 18 ciki har da Denis Mukwege, da ya lashe lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel a shekara ta 2018.