1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kwashe kwanaki 100 bayan kutsen Rasha a Ukraine

June 3, 2022

Yayin da ake ci gaba da lalubo hanyoyin kawo karshen yakin Rasha da Ukraine, a wannan Juma'a aka cika kwanaki 100 da fara yakin, da ya haifar da tsadar kayayyakin abinci a duniya.

https://p.dw.com/p/4CEPJ
Ukraine Russland Konflikt | Donbass-Region
Hoto: Alex Chan/ZUMA Wire/IMAGO

Hakan na zuwa ne yayin da gwamnatin Kyiv ta sanar da cewa Moscow a yanzu ta kwace ikon yankuna 5 ciki har da yankunan Crimea da wasu sassan Donbas da ta kwace a shekarar 2014. 

A yanzu haka, dakarun Rasha sun mayar da akalarsu wajen kwace ikon gabashin Ukraine, yayin da ake gargadin yakin ya dauki karin wani lokaci.

Da yake yi wa 'yan majalisar dokokin Luxembourg jawabi, shugaba Volodmyr Zelensky na Ukraine ya ce kimanin kashi 20 cikin dari na yankunan kasar na karkashin ikon Rasha, ba ya ga dakaru kimanin 100 da ke mutuwa a kullum a fagen yaki, batun da babban sakataren kungiyar kawacen tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ke cewa, akwai bukatar kawayen Ukraine su sake daura damara wajen kawo yakin. 


Alkalumma na nuni da cewa, dubban mutane sun rasa rayukansu yayin da wasu miliyoyi suka tsere daga kasar tun bayan da Rasha ta kaddamar da mamaya a Ukraine a ranar 24 ga watan Fabarairun da ya gabata.