1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya na tattaunawa kan Siriya

January 27, 2012

Rasha ta sanar da cewar ba za ta amince da ƙudirin MDD akan Siriya inda Majalisar ta buƙaci shugaban ƙasar Siriya ya yi marabus

https://p.dw.com/p/13sDC
Baschar Al Assad Shugaban ƙasar SiriyaHoto: picture-alliance/abaca

Ƙasar Rasha ta ce ba za ta goyin bayan ƙudirin kwamitin sulhu na MDD akan siriya;da yake magana da manema labarai ƙaramin ministan harkokin waje na rashan Guennadi Gatilov.

Ya ce ko ƙadan ba su amince da yunƙurin Majalisar ba na warwware rikicin na Siriya ta hanyar yin kira ga shugaba Bashar Al- Assad da ya yi marabus.Kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniyar na tattaunawa domin yanke muhiman shawarwari akan ƙasar ta Siriya.kuma nan gaba aka shirya ƙungiyar ƙasashen laraba zata yi wata ganawa akan batun a birnin New York .Haɗin gwiwar ƙungiyoyin kare hakin jama'a na ƙasar ta Siriya sun sanar da cewa mutane 62 suka mutu a hare haren da jami'an tsaro suka kai a garuruwan Homs da Hama da kuma Idleb a yan kwanakin baya baya nan.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman