1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kurdawa sun amince a yi sulhu

July 28, 2018

Mayakan Kurdawa a Siriya, sun ce sun amince da zama kan teburin tattaunawa da gwamnatin kasar don kawo karshen zubar da jini.

https://p.dw.com/p/32EyP
SDC Syrian Democratic Council
Hoto: Getty Images/AFP/D. Souleiman

A cewar Kurdawan za a kafa wasu kwamitoci ne da za su tsara taswirar kyautata kasar da ta rarrabu ta bangaren shugabanci da kuma madafun iko.

Kamar yadda bangaren jagorancin Kurdawan ya sanar, Siriya ce ta kira wannan zama na tattaunawa.

Gwamnatin Shugaba Bashar al Assad da ke samun goyon bayan Rasha dai, ta yi nasarar karbe kusan dukkanin yankunan da a baya ke hannun mayakan na tawaye.

A share guda kuwa wannan labarin na aza tambayoyi kan manufofin Amirka a Siriya, ganin yadda kasar ta aika sojoji musamman a yankunan da ke hannun mayakan na Kurdawa lokacin da ake yaki da kungiyar IS.