1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyoyi sun damu kan komawar 'yan hijira Najeriya

April 29, 2022

Kungiyoyin agaji na nuna damuwa game da komar da wasu 'yan Najeriya da suka tsere wa rikici gidajensu na asali a jihar Borno, bayan kwashe lokaci a Jamhuriyar Nijar.

https://p.dw.com/p/4Ad5m
Symbolbild I Nigeria I Islamisten nehmen Geiseln
Hoto: Getty Images/AFP/Stringer

Akalla 'yan Najeriya dubu hudu ne suka koma gida, bayan tserewa da suka yi cikin shekarun da suka gabata, inda suka fake a makwabciya Jamhuriyar Nijar.

Dubban mutanen da suka koma duk da rashin tabbas game da halin tsaro, sun tsere wa mazunansu ne da ke cikin jihar Bornon da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Galibin su dai sun fito ne daga yankunan Malam Fatori da ke a gundumar Abadam da suka yi ta fama da hare-haren kungiyoyi masu da'awar jihadi.

Komawar tasu gida, na da alaka kai tsaye ne da tsayuwar da hukumomi suka yi na ganin an rufe sansanonin da ke dauke da dubban masu zaman hijira.

Kungiyoyin agaji dai na nuna fargabar yiwuwar maida mutanen cikin hadari, ganin cewa har yanzu ana samun hare-hare a yankunan da suka bari sama da shekaru biyar.