1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha da kasashen Larabawa na neman tsagaita wuta a Gaza

Zainab Mohammed Abubakar
December 20, 2023

Rasha da kungiyar kasashen Larabawa sun jaddada bukatar zartar da kudurin tsagaita wuta na MDD kan yakin Isra'ila da Hamas, a yayin taron hadin gwiwar Rasha da Larabawa a birnin Marrakesh na kasar Morocco.

https://p.dw.com/p/4aQ51
Hoto: Abed Rahim Khatib/dpa/picture alliance

Taron da ke gudana a karkashin jagorancin ministan harkokin wajen Morocco Nasser Bourita, ya samu halartar ministan harkokin wajen Rasha Lavrov da jami'an diflomasiyya na kungiyar kasashen Larabawa mai mambobi 22, da ya kuma ya mayar da hankali kan rikicin Gaza.

A wannan Larabar ce ake saran kwamitin sulhu na MDD zai kada kuri'a kan wani kuduri da ke neman a dakatar da rikicin, kamar yadda wasu majiyoyin diflomasiyya suka shaida.

Yakin da Isra'ila ke yi a Gaza ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan dubu 20, akasari mata da kananan yara, a cewar ma'aikatar lafiyar yankin na Falasdinu da ke karkashin ikon Hamas.

A ranar 7 ga watan Oktoba, mayakan Hamas sun kai wani hari da ba a taba ganin irinsa ba a kan Isra'ila daga Gaza, inda suka kashe mutane kusan 1,200, galibi fararen hula, a cewar alkaluman hukumomin na Isra'ila.