1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kungiyar kasashen Gabashin Afirka ta janye sojoji daga Congo

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
December 3, 2023

Shugaba Felix Tshisekedi ya zargi dakarun kungiyar da kulla alaka da 'yan tawayen M23

https://p.dw.com/p/4Zihj
Hoto: Alexis Huguet/AFP

Kungiyar raya kasashen Gabashin Afirka EAC ta fara janye dakarun tsaronta daga Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo da safiyar Lahadin nan, sakamakon yadda Congon ta gaza sabunta yarjejeniyar da suka kulla ta wanzar da zaman lafiya a kasar, mai fama da rikicin 'yan tawayen kungiyar M23.

Karin bayani:Boren adawa da Ruwanda a DR Congo

Tun a cikin watan Nuwamban da ya gabata ne EAC ta kai dakarunta kasar ta Congo bayan gayyatarta da kasar ta yi don murkushe 'yan tawayen, to sai dai daga baya shugaba Felix Tshisekedi ya zargi dakarun kungiyar da kulla alaka da 'yan tawayen M23, maimakon kokarin kawar da su.

Karin bayani:DR Congo: 'Yan bindiga sun kashe mutane 30

Rukunin farko na sojojin taron dangin guda 100 da suka fito daga kasashen Kenya da Uganda da Burundi da kuma Sudan ta Kudu, sun bar filin jirgin saman birnin Goma da asubashin Lahadi sannan suka sauka a Nairobi babban birnin kasar Kenya.