Kungiyar IS ta ci kasa a birnin Rakka
October 18, 2017Kungiyar 'yan jihadi ta IS ta rasa babban birninta a Siriya wato Rakka wanda a ranar Talata mayakan Kurdawa da na Larabawa da rundunar kawancen da Amirka ke jagoranta da marawa baya suka yi nasarar kwato birnin baki dayansa daga hannun 'yan jihadin bayan fafatawa ta tsawon watanni hudu. Tuni dai mayakan suka fantsama a titunan birnin inda suke nuna murnarsu ga wannan nasara da suka samu.
Kwace birnin Rakka da ke a matsayin cibiyar kungiyar ta IS a kasar Siriya, ba karamin koma baya ba ne ga 'yan kungiyar da suka yi ruwa suka yi tsaki a 'yan shekarun da suka gabata a kasashen na Siriya da ma Iraki inda suka mamaye manyan yankuna tun daga shekara ta 2014. Mayakan da Amirka ke marawa baya sun daga tuta a filin nan da ake kira Filin Rakka, da kuma filin Al-Naeem, da ke nuni da cewa a halin yanzu birnin da aka ragargaza ya fita daga karkashin ikon mayakan jihadin na kungiyar IS. Mai magana da yawun mayakan da suka kwaci birnin na Rakka Talal Sello, ya ce wannan fafatawa ce da aka yi gumurzu da mayakan sakan:
" Rakka ya fada a karkashin kulawarmu yanzu haka. Amma dai wannan fafatawa ta kawo karshe, sai dai kuma abun da zamu yi nan gaba shi ne bincikawa gida-gida domin ko zamu gano wasu ababe masu fashewa da suka bari, ko mu samu wasu mayakan na IS da suka buya."
Sai dai kuma samun birnin na Rakka ya wakana ne yayin da yakin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 3,250 cikinsu fararan hula 1,130 kananan yara ma dai da suka mutu a kokarin kwato birnin na Rakka sun kai 270, yayin da adadin mayakan na bangarorin biyu da suka mutu ya kai na mutane 2,120 a cewar kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin bil-Adama ta kasar ta Siriya da ke da cibiya a birnin London.