SiyasaJamus
Kungiyar IS ce ta kai hari a Afghanistan
October 8, 2021Talla
Cikin wata sanarwar da kungiyar ta fitar ta kafar Telegram, ta ce wani mayakinta ne ya kai harin na kunar bakin wake a masallacin na 'yan Shi'a.
Harin wanda aka kai kan masallatan da ke sallar Juma'a, ya haklaka akalla mutum 60 wasu sama da 140 suka jikkata.
Wasu hotunan bidiyo sun nuno yadda harin na bom ya tarwatsa masallacin, tare da gawarwakin jama'a da babu dadin kallo.
Asibitocin yanki ma dai sun cika makil da mutanen da ke neman dauki na gaggawa.
Gwamnatin Taliban da ke jagorantar al'amura a Afghanistan dai na fama da tarin matsaloli, ciki har da tsananin barazana daga mayakan na IS.