1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tabo bakin haure 50 daga Sahara

Abdoulaye Mamane Amadou
September 13, 2022

An ceto rayukan mata da kananan yara 50 da suka bata a hamadar Sahara a Jamhuriyar Nijar a yayin da suke kokarin tsallakawa ta barauniyar hanya zuwa kasar Libiya

https://p.dw.com/p/4Gn0l
Libyen l Migration l Flüchtlinge aus Niger  in Misrata
Hoto: Mahmud Turkia/AFP via Getty Images

Kungiyar  kula da kaurar jama'a IOM ta ce galibi wadanda aka ceto sun bata ne a yayin da suke kokarin dawowa daga Libiya, ko da yake hukumar ta ce akwai kuma wasu kuwa da ke kan hanyar shiga kasar Libiyar ta barauniyar hanya.

Mutane 49 daga cikin 50 din da aka ceta bayan sun makale a hamadar yankin Dirkou 'yan Najeriya ne, sai kuma wani mutun dan Kamaru daya in ji hukumar IOM.

Yanzu haka mutanen na samun kulawa daga mahukuntan yankin Agadez da ke arewacin Nijar tare da tallafin hukumar ta IOM.