1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar EU da IAEA akan rikicin Nukiliyan Iran

Zainab A MohammadMay 12, 2005

Rikicin Nukiyan Iran na neman daukan wani salo

https://p.dw.com/p/Bvc0
Hoto: AP

Bisa dukkan alamu Iran zata bawa turai dama ta karshe na tattaunawa,kafin ta koma sarrafa sinadran Uranium dinta data dakatar sakamakon matsin lamba,wanda Washinton tace zaa iya amfani dashi wajen kera makaman Nuclear.

Tun da safiyar yau ne wata majiyar diplomasiyya dake hukumar yaki da yaduwar makaman nuclear ta Mdd dake da matsuguninta a Vienna,tace ana kyatata zaton samun wasika daga babban jagoran wakilan Tehran kan wannan batu Sirus Naseri,wasikar da zata sanar da matsayinsu na komawa cigaba da sarrafa sinadran atom domin samara da wutan lantarki a kasar.

Hakan dai na iya kawo karshen tattaunawan da kasashen Faransa,Britania da Jamus keyi da Tehran din,domin marawa kiran da Amurka tayi na gurfanar da Iran din gaban komitin sulhun majalisar dunkin duniya,tare da kakaba mata takunkumin tattalin arziki dana wasu harkoki da kasashen ketare.

Sai dai a hannu guda kuma wata majiya na nuni dacewa babu alamun gabatar da wannan wasika ayau.Da manema labaru suka nemi jin ta bakinsa,Naseri yaki cewa komai dangane sako zuwa ga shugaban hukumar ta IAEA Mohammed Elbaradei.

Majiyar dake kusa da tattaunawan kungiyar ta Eu da Iran din dai ta sanar dacewa,hukumomin Iran sun gudanar da tarurruka na gaggawa da wakilan turan a asirce a yan kwanakin da suka gabata.Abunda ake ganin cewa zai taimaka wajen warware wannan rikici daya barke tun a watan Nuwamba,wanda kuma ke neman daukan wani salo.

Amurka dai tayi imanin cewa Iran din na kokarin sarrafa makamai Nuclear da harkokinta na sinadaran atom,da tace na makamashine,kuma Amurkan ta bukaci a gurfanar da Iran gaban komitin sulhun mdd mai wakilai 15.Kungiyar gamayyar turai Eu dai na kokarin ganin cewa Iran din ta dakatar da duk wasu harkokinta da suka shafi wannan zargi da amurkan ke mata.

Britania da faransa da Jamus dake jagorantan Turai a wannan tattaunawa a wata wasika da suka aike, sun gargadi Tehran data guji dukkan wani mataki na komawa sarrafa sinadaran tan a Atom,domin hakan zai kai tag a hukunci.Wasikar wadda aka aikewa shugaban hukumar tsaron Iran Hassan Rouhani jiya laraba,ya harzuka Tehran inda tayi watsi da sanarwa hukumar makamashin Nuclear ta IAEA halin da take ciki.

Wani jamiin diplomasiyyan Iran din ya fadawa manema labaru cewa gwamnatinsu na laakari da bukatun komawa kan teburin tattaunawa da aka gabata musu a wannan wasikar cikin makonni biyu masu gabatowa,domin tattauna halin da ake ciki.Kasashen duniya dai sun bayyana tsoronsu dangane da wannan kera makaman Nuclear da ake zargin Iran dayi.

A watan Nuwamban bara nedai Iran ta cimma yarjejeniya da Britania da Faransa da Jamus ,na dakatar da sarrafa sinadran uranium.Amma ayau Iran tace zata cigaba da wasu harkokinta na sarrafa sinadran na Uranium.

Wasikar gargadin turan wadda ministocin harkokin wajen kasashen Jamus da Britania da Faransa suka rattaba hannu,na nuni dacewa idan har iran ta karya wannan kaidoji da aka cimm a baya,babu shakka zata ruguza dukkan wani yunkuri na tattauna yiwuwan warware wannan matsala,abunda kuma a daya hannun ke nufin gurfanar da ita gaban komitin sulhun mdd.