1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar EU ta kulla wata yarjejeniyar rigakafin COVID-19

Zulaiha Abubakar
June 13, 2020

Kasashen Jamus da Faransa da Italiya sun rattaba hannu a yarjejeniya da kamfanin samar da magunguna na AstraZeneca, domin wadata kasashen kungiyar EU da rigakafin Coronavirus aikin dai zai lakume makudan kudade.

https://p.dw.com/p/3djTk
Logo des Pharmakonzerns AstraZenica
Hoto: Andrew Yates/AFP/Getty Images

A shekara ta 1999 ne kasashen Birtaniya da Sweden suka hada karfi wajen kafa kamfanin magungunan na AstraZeneca wanda ya yi fice wajen samar da rigakafin cututtuka a kasashen, sanarwar ta kara da cewar ana sa ran kamfanin zai kammala aikin samar da rigakafin nan da karshen wannan shekara tare da daukar alwashin wadata kasashen kungiyar ta EU wadanda suka zabi shiga aikin samar da rigakafin annobar COVID-19 wacce ta haifar da tsaiko a mafiya yawan kasashen duniya

Wata kididdigar hukuma ta nunar da cewar akwai akalla mutane miliyan 447 a kasashen kungiyarta EU kuma tuni hukumar zartaswar kungiyar ta bukaci kasashen su hanzarta shiga cikin wannan yarjejeniyar samar da rigakafi domin su ribaci samun rigakafi cikin sauki a nan gaba.