Boko Harm ta hallaka sojojin Chadi 24
August 5, 2021Talla
Harin ya afku ne a tsibirin Tchoukou Telia da ke da nisan kilomita 190 daga arewa maso yammacin birnin Ndjamen babban birnin kasar. Wani kantoma a yankin na tafkin chadin Haki Djiddi, ya ce sojojin gwamnatin sun dawo daga sinitinri suna cikin hutawa kan hanya a sa'ilin da 'yan Boko Haram din suka afka musu. A halin da ake ciki gwamnatin Chadi ta ce ta tura karin sojoji a yankin domin bin sawun maharan.