1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kundancin Sudan ta rantsar da Majalisar Dokokinta

August 6, 2011

Kudancin Sudan ta rantsar da 'yan majalisan dokokin ta a yau asabar, wuni biyu kafin ƙaddamar da zaman farko na Majalisar

https://p.dw.com/p/12CMJ

Kakakin majalisar dokokin, Honourable Igga ya yi kira da su bada haɗin kai domin cigaban ƙasa ba tare da la'akari da banbance-banbancen asali ko kuma jamiyyun siyasa ba.

Bisa tanadin dokar da fadar shugaban ƙasa ta bayar ranar litinin da ya gabata, majalisar ta ƙunshi 'yan majalisa guda 170 waɗanda aka zaɓa tun kafin ƙasar ta sami 'yancin kai da kuma wasu 96 daga waɗanda aka zaɓa su wakilci yankunan kudancin ƙasar lokacin da suke ƙarƙashin gwamnati a Khartoum sai kuma wasu 66 da aka zaɓa daga baya.

Daga cikin mambobin guda 332 waɗanda aka zaɓa an rantsar da 279 a yau a ciki har da mataimakin shugaban ƙasa Riek Machar.

Shugaba Salva Kiir bai samu kasancewa a bukun rantsarwar ba. Ana sa ran sabuwar majalisar zata fara aiki ranar litini domin ta maye gurbin gwamnatin wucin gadin da ke ci.

To sai dai jagorar adawar ƙasar Onyoti Adigo daga jamiyyar Democratic Change wadda ta ɓalle daga jamiyya mai ci ta SPLM ya kushe yawan wakilan da ke majalisar yana kira da a rage yawan su.

Mawallafiya: Pinado Abdu

Edita: Zainab Mohammed Abubakar