1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kudancin Sudan ya zama ƙasa 'yantatta

February 7, 2011

Kashi kusan 99 daga cikin 100 na waɗanda suka kaɗa ƙuri'a a zaɓen raba gardama na kudancin Sudan sun amince yankin su ya zama ƙasa mai cin gashin kai. Tuni shugaba Al Bashir ya yi na'am da sakamakon.

https://p.dw.com/p/10CZ9
Alamar tutar sabuwar ƙasar Kudancin SudanHoto: DW/Schlindwein

Shugaba Umar Hassan Al Bashir na Sudan ya amince da sakamakon zaɓen raba gardama da ya bai wa yankin kudanci damar zama ƙasa mai cin gashin kanta. A lokacin da ya ke jawabi ga al'umar ƙasarsa ta kafar talabijin tun ma kafin a wallafa sakamakon, Shugaba Al bashir ya ce gwamantinsa za ta mutunta zaɓin da 'yan asalin yankin suka yi wa kansu. Yarjejniyar wanzar da zaman lafiya da ɓangarorin biyu suka cimma domin juya babin yaƙin basasa da kudancin ya fiskanta ne ya taimaka aka gudanar da wannan ƙuri'a ta jin ra'ayin jama'a.

Alƙaluman da hukumomin da alhaki ya rataya musu a wuya suka wallafa, sun nunar da cewa kusan kashi 99 daga cikin 100 na al'umar yankin sun zaɓi ɓallewa daga gwamnatin tsakiya domin samun cikakken 'yanci. Sai dai masana na nuna damuwa dangane da ƙalubale da jaririyar ƙasar za ta fiskanta nan gaba, kama daga na ƙabilanci, har i zuwa na rabon arzikin man fetur da Allah ya hore wa ƙasar.

Ɗaruruwan 'yan kudancin Sudan ne suka hallara a Juba babban birnin ƙasar domin sheƙe ayarsu dangane da cimma ruwa da haƙarsu ta samun ƙasa ta kansu da ta yi. 'Yan yankin kudancin Sudan suna ɗaukar ɓallewar a matsayin martani ga gallazawa da suka fiskanta a shekaru 20 ƙarƙashin gwamnatin dunƙulalliyar ƙasar Sudan.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Halima Balaraba Abbas