1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An dage shirin zaben shugaban Aljeriya

Yusuf Bala Nayaya
June 2, 2019

Gangamin adawa dai da gwamnatin Shugaba Bouteflika ya sa ya sauka daga mulki a watan Afrilu bayan shekaru 20, duk kuwa da rashin lafiya da shugaban yake fama.

https://p.dw.com/p/3JdfH
Algerien, Algier: Erneute Proteste gegen die Regierung
Hoto: picture-alliance/dpa/B. Bensalem

Kotun koli ta tsarin mulkin kasar Aljeriya a wannan Lahadi ta bayyana cewa abu ne da ba zai yiwu ba a gudanar da zaben da zai maye gurbin Shugaba Abdelaziz Bouteflika kamar yadda aka tsara yi a ranar hudu ga watan Yuli mai zuwa.

A cikin wata sanarwa da kotun tsarin mulkin ta fitar a Lahadin nan, ta ce yanzu ya rage ga shugaban rikon kwarya Abdelkader Bensalah ya sa wata sabuwar rana da za a gudanar da zaben kasancewar biyu cikin 'yan takarar ma ba a tantance su ba.

Gangamin adawa dai da gwamnatin Shugaba Bouteflika ya sa ya sauka daga mulki a watan Afrilu bayan shekaru 20.
Tun dai a watan Fabrauiru ne dubban al'ummar Aljeriya suka tattaru a birnin Algiers da wasu birane don yin babban gangami na adawa da takarar Bouteflika a zaben da aka tsara yi 18 ga watan Afrilu. Inda masu adawar ke cewa babu batu na neman mulki a wa'adi na biyar ga shugaban da aka zaba tun a shekarar 1999.