1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun ICC za ta tuhumi Saif -Al-Islam

October 30, 2011

Kotun duniya da ke hukumta manyan laifuka na yaƙi ta ce ta na da shedu akan kisan ƙare dangi da ɗan kanar Gaddafi ya aikata a Libiya

https://p.dw.com/p/131vb
Luis Moreno Ocampo,Shugaban Kotun ICCHoto: dapd

Babban lauya mai gabatar da ƙara na kotun duniya da ke hukumta manyan laifuka na yaƙi wato Luis Moreno Ocampo ya ce suna da ƙwaƙwaran shedu waɗanda ke tabbatar da cewa ɗan kanar Gaddafi Saif-Al-Islam ya na da hannu dumu dumu a cikin kisan kiyasun da sojojin tshohuwar gwamnatin Libiya ta aikata akan fararen fula. Ocampo wanda ke yin magana da kamfanin dilacin labarai na Reuters a birnin Bejin inda yake yin ziyara ya ce suna da wani sheda wanda ya baiyana masu yadda ɗan Gaddafin ya riƙa ɗaukar sojojin haya na ƙasashe daban daban.

Ya ce ko da shi ke ya ce bai aikata lafi ba, amma ya ce alƙali ne kawai zai iya tabatar da haka indan har ya baiyana a gabansa. Saif Al Islam dai ya samu arcewa daga Libiyar tun bayan mutuwar mahaifin sa, kuma kotun ta ICC na neman sa ruwa jallo akan tuhumar da take yi masa na aikata kisan ƙare dangi. Kawo yanzu akwai rahotanin dake nuni da cewa ya samu mafaka a cikin hamadar Tenere ta Nijar inda tsofin mayaƙan kungiyar 'yan tawaye ta Abzinawa ke yi masa goma ta arziki.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Ahmad Tijani Lawal