1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun ICC da batun laifukan yaƙi a Ruwanda

January 26, 2011

Wani jigo a ƙungiyar 'yan tawayen Ruwanda yana fuskantar tuhuma a gaban kotun ICC da ke birnin The Hague

https://p.dw.com/p/103Fh
Zaman taron hukumar gudanarwar kotun ICC a birnin The Hague, Litinin 6 - Satumba 2004.Hoto: AP

Wani jagoran 'yan tawayen ƙasar Ruwanda, wanda aka zarga da laifin yin kissar kiyashi da kuma fyaɗe a ƙasar, a yanzu an miƙa shi ga kotun ƙasa da ƙasa dake hukunta masu aikata manyan laifukan yaƙi da ke birnin The Hague. Callixte mmbaruush - Immana, wanda aka kwatanta da cewar babban jigo ne a ƙungiyar 'yan tawayen FDLR ta ƙasar Ruwanda, tun cikin watan Oktobar bara ne aka tsare shi a birnin Paris na ƙasar Faransa bayan wani sammacin cafke shi da aka bayar bisa zargin kissar kiyashi da kuma fyaɗe. Kotun ta ICC ta ce mm-baruush - immana yana da hannu dumu - dumu cikin kisar ƙare dangin da aka yi a Ruwanda cikin shekara ta 1994, kana ya aikata kissa da kuma fyaɗe, waɗanda suka janyo yaƙe-yaƙe a ƙasar Kongo. Tsareshin dai ya biyo bayan binciken da ƙasashen Jamus da Faransa da Kongo da kuma Ruwanda suka yi ne. Wani kakakin kotun da mazaunin ta ke birnin The Hague ya ce a wannan Jumma'ar ce za'a yi zaman share fagen sauraren shari'ar ko da shike kuma - kamar yadda ya ce ba'a sanya ranar sauraren ƙa'rar baki ɗaya ba.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu