1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun Burundi ta ce a rantsar da shugaban kasa

June 12, 2020

Hukumomi a Burundi, sun bukaci a yi duk wani mai yiwuwa don samar da sabon shugaban kasar, bayan mutuwar shugaba mai barin gado cikin 'yan kwanakin da suka gabata.

https://p.dw.com/p/3dhp9
Burundi Bujumbura Verfassungsrichter
Hoto: Getty Images/AFP/T. Nitanga

Kotun tsarin mulki a Burundin, ta bukaci da rantsar da zabebben shugaban kasar ba tare da wani bata lokaci ba, saboda kawo karshen kila-wa-kala da mutuwar marigayin Shugaba mai barin gado, Pierre Nkurunziza a farkon wannan mako.

Cikin watan jiya ne dai 'yan Burundi suka zabi Evariste Ndayishimiye a matsayin shugaban kasa, sai dai mutuwar Nkurunziza da da hukumomi suka danganta da bugun zuciya, na kokarin bai wa kakakin majalisar dokokin kasar kuma na hannun daman marigayin, damar jagoranci na riko.

Bisa tsarin mulkin kasar dai, sai a ranar 26 ga watan Agusta ne za a rantsar da zababben shugaban, amma majalisar ministocin Burundin suka bukaci shawarar kotun na tsarin mulki a jiya Alhamis.