1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Kotun Pakistan ta yi da tuhumar tsohon firaminista

Suleiman Babayo AMA
November 29, 2023

Wata babbar kotun Pakistan ta wanke tsohon firaminista Nawaz Sherif kan laifin da ake tuhume shi na cin hanci da rashawa tare da iyalansa.

https://p.dw.com/p/4ZaUJ
Pakistan, Lahore | Tsohon Firaminista Nawaz Sharif na Pakistan
Tsohon Firaminista Nawaz Sharif na PakistanHoto: Ali Kaifee/DW

Wata kotu a kasar Pakistan ta yi watsi da laifin da aka samu tsohon Fairaministan kasar Nawaz Sharif na cin hanci, kamar yadda lauyansa ya bayyana. A shekara ta 2018 aka samu Sharif da laifi kan tuhumar cin hanci tare da iyalansa sakamakon wasu gidaje da suka saya a birnin London na Birtaniya, abin da ya saka aka daure shi na tsowon shekaru 10.

Wata babbar kotu da ke birnin Islamabad fadar gwamnatin kasra ta wanke tsohon Firaministan Nawaz Sharif.

A wani labarin kuma tsohon Fiaminista Imran Khan na kasar ta Pakistan da yanzu haka yake daure, ya amince daya daga cikin lauyoyinsa ya tsara wa jam'iyyarsa ta PTI takara na mukamun firaminista zaben da ke tafe, lamarin da ya tabbatar da cewa lauyan Gohar Khan ke zama dan takara kan neman firamnista a jam'iyyar PTI.