1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta daure wasu manya a Burkina Faso

September 2, 2019

Wata kotun soji a Burkina Faso, ta yanke wa wasu na kusa da hambararren shugaban kasar Blaise Campaore hukuncin dauri saboda samunsu da laifuka masu nasaba da kifar da gwamnati.

https://p.dw.com/p/3Ou5Z
Djibril Bassole tare da Janar Gilbert Diendere
Djibril Bassole tare da Janar Gilbert Diendere

Kotun sojin ta yanke wa Gilbert Diendere wanda babban na hannun daman tsohon Shugaba Campaoren ne daurin shekaru 20 a gidan yari yayin da shi kuwa Djibril Bassole, ya sami daurin shekaru 10.

A shekara ta 2014 ne masu zanga-zanga suka kifar da gwamnatin tsohon Shugaban Blaise Campaore wanda ya kwashe shekaru 27 yana mulki a Burkina Faso, abin ma da ya tilasta masa tserewa daga yankin Afirka ta Yamma.

Kotun ta soji da ke Ouagadougou babban birnin kasar ta ce ta sami Gilbert Diendere wadan Janar ne na soja, da laifin kisan kai da kuma barazana ga tsaron kasa.

Akalla dai mutum 14 suka mutu lokacin yamutsin a shekaru biyar da suka gabata, wasu sama da mutum 250 kuwa suka jikkata.