1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukuncin daurin rai da rai kan mutane 500

Abdul-raheem Hassan
November 26, 2020

Hukuncin na daurin rai da rai, ya kawo karshen shari'ar da ake wa mutanen 500 a kan zarginsu da hannu a yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Erdogan a 2016.

https://p.dw.com/p/3lqLN
 Recep Tayyip Erdogan
Hoto: Getty Images/AFP/A. Altan

Shari'ar ta shafi wasu sojoji da ake zargi da kitsa juyin mulkin a cikin barikin sojoji, tare da ba da umarnin jefa bude wuta a gine-ginen gwamnati. Akalla mutane 251 sun mutu sama da 2,000 sun jikkata a yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba.

Mutane 385 sun ba da sheda a shari'a 515 tun bayan fara shari'ar, an yankewa mutane sama da 200 hukuncin daurin rai da rai a gidan kaso, wadanda ake zargin suna da alaka da malamin addinin kasar Fethullah Gülen da ake zargin shi ya shirya juyin mulkin.