1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Bajamushe ya taimaka wa kungiyar IS kisan kai

November 27, 2021

Wata kotu a birnin  Düsseldorf na Jamus ta yanke wa wani matashin Bajamushe zaman shekaru 10 a gidan kaso bayan samunsa da laifi mai nasaba da kisan kai.

https://p.dw.com/p/43Yxv
Düsseldorf | Urteilsverkündung im Mordprozess gegen den IS-Terroristen Nils D.
Hoto: Oliver Berg/dpa/picture alliance

Kotun ta samu Bajamushen da laifin shiga kungiyar ta'addanci ta IS, inda ya yi amfani da wannan damar ya taimaka wurin gallaza wa wasu mutane da IS ta tsare a wani garin kan iyakar Siriya da Turkiyya, lamarin da ya yi ajalin mutane uku  a shekara ta 2014.


Masu shigar da kara sun so a yanke wa Bajamushen mai suna Nils D. daurin rai-da-rai amma kotun ta Jamus ta ce ta sassauta masa saboda bai wahalar da shari'a ba a wurin bayar da bayanan ta'addanci.


A shekara ta 2014 dai daruruwan Jamusawa ne suka dauki kayansu suka tafi Siriya, inda suka shiga kungiyar IS wace ta so kafa Daula a Siriya. A baya-bayan nan hukumomin Jamus na kokarin ganin sun hukunta Jamusawan da suka shiga IS da yanzu haka ake rike da su a kasashen  Siriya da Iraqi.