1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu a Ghana ta yi watsi da matakin rufe majalisar kasar

October 31, 2024

Kotun kolin Ghana ta yi watsi da matakin da ya sanya aka rufe majalisar dokokin kasar, gabanin babban zaben kasar da zai gudana a watan Disambar 2024.

https://p.dw.com/p/4mQOh
Mahamudu Bawumia da kuma John Dramani Mahama
Mahamudu Bawumia da kuma John Dramani MahamaHoto: NIPAH DENNIS/AFP/Getty Images | OLYMPIA DE MAISMONT/AFP

 A makon da ya gabata ne shugaban majalisar, Alban Bagbin ya ce akwai kujeru hudu a majalisar da ba su da wakili. Babban alkalin kotun, ya ce idan aka yi la'akari da irin barnar da hakan zai yi ga mazabu da ke da dubun dubatar al'umma, ya zama wajibi kotu ta gaggauta magance wannan takaddama.

Karin bayani: Dambarwar siyasa a majalisar dokokin Ghana

Rikici ya kaure ne a tsakanin jam'iyyar shugaban kasar, Nana Akufo-Addo ta NPP da kuma jami'iyyar adawa ta NDC wadda ta samu karamin rinjaye bayan da wasu 'yan majalisu hudu suka sauya sheka. Kundun tsarin mulkin Ghana dai bai ba 'yan majalisa damar sauya sheka daga jam'iyyar da aka zabe su ba.

Ana dai ganin kasar Ghana a matsayin kasar da ke da saukin rikicin siyasa a yankin Yammacin Afirka da ke fama da tarin rikice-rikice.