1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu a China ta zartar da hukunci kan wani fitaccen lauya

December 22, 2006
https://p.dw.com/p/BuWg

Wata kotun kasar China ta zartas da hukuncin dauri na shekaru 3,kan wani shahararen lauya dan kasar mai paputukar kare hakin yan adam Gao Zhisheng.

Mahukuntan kasar ta China dai suna zargi Mr.Gao ne da laifin bata sunan kasar,wanda suka bayyana yayi ne wajen wallafa batutuwa kan siyasa ta yanar gizo ta internet da kasashen ketare.

Kotun har ila yau ta hana mr.Gao damar nua kin amincewa a kann wannan hukunci.

Mr.Gao Zhisheng yana tsare ne tun watan Agusta lokacin da gwamnatin ta tashi kann lauyoyi kamarsa.