Koriya ta arewa tayi Allah wadai da atisayen sojin Amurka da na koriya ta kudu
March 27, 2006Talla
Kasar Koriya ta arewa tayi Allah wadai da atisayen shekara shekara tsakanin sojojin Amurka dana Koriya ta kudu,tana mai gargadin cewa,ba zasu ji dadin abin da zai biyo baya ba hakazalika kuma,ba kasar Amurka ce kadai take da ikon kai hari akan kowace kasa daga dama ba.
Gwamnatin Koriya ta arewan tace,wannan atisaye da suka fara tun ranar asabar,wani yunkuri ne ko kuma bita na neman mamaye ta.
Wata jaridar kasar ta buga a sharhinta cewa,kasar Amurkan ta kuka da kanta,bisa duk wani sakamako daka iya biyo bayan wannan atisaye.
Kimanin dakarun Amurka 25,000 dana Koriya ta kudu da baa san adadinsuba suke wanna atisaye,da suka baiyana cewa na matakan tsaro ne.