1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa ta yi harbe-harben rokoki

Abdoulaye Mamane Amadou
May 4, 2019

Koriya ta Arewa ta yi wani gwajin rokoki masu cin gajeren zango a tekun Japan a wannan rana ta Asabar kamar yadda ma'aikatar tsaron kasar Koriya ta Kudu ta bayyana.

https://p.dw.com/p/3Hv1w
Nordkorea, Raketen, Abschuss, Manöver, Japanisches Meer
Hoto: picture-alliance/dpa

Ma'aikatar tsaron Koriya ta Kudu ta ce Koriya ta Arewa ta yi gwajin wasu rokoki masu cin gajeren zango da suka yi tafiyar kilo mita 70 zuwa 200 a gabar garin Wonsan Arewa maso gabashin kasar. Wannan gwajin na zuwa ne a daidai lokacin da duk wata tattaunawa tsakanin gwamnatin Pyongyang da ta Amirka ta tsaya game da batun kwance damarar Nukiliyar kasar ta Koriya. 

Ko a watan jiya ma hukumomin kasar Koriya ta Arewa sun bayyana gwajin wani makamakin Nukilya, duk yake ba su bayyana mizanin makamin ba. Gwamnatin Koriyar ta Arewa ta gargadi Amirka da cewa zata ga mummunan sakamako muddin ba ta sassauto daga matsayinta game da batun makamai masu linzamin kasar ba.