1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pyongyang na zargi MDD na taimakon Amirka

Abdul-raheem Hassan
August 14, 2022

Koriya ta Arewa ta caccaki Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, kan kalaman da ta kira 'masu hatsarin gaske' na neman kawar da makaman kare dangi na Pyongyang.

https://p.dw.com/p/4FVgp
Koriya ta Arewa
Hoto: KCNA/REUTERS

Guterres, wanda ya kai ziyarar kwanaki biyu a Koriya ta Kudu, ya bayyana cewa babban aikin da ke gabansa shi ne kawar da makaman nukiliyar Koriya ta Arewa don samar da zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali a yankin baki daya.

Sai dai ma'aikatar harkokin wajen Koriya ta Arewa, ta zargi MDD da yunkurin kare muradun Amirka. Koriya ta Arewa ta yi gwajin makaman da ba a taba gani ba a bana, wanda ya hada da harba makami mai linzami da ke tsakanin nahiyoyi a karon farko tun shekarar 2017.