1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Koriya ta Arewa ta sabunta aniyar kai hare-hare

March 27, 2021

Koriya ta Arewa ta yi barazanar karfafa gwaje-gwajen manyan makamanta, wani martani na farko da kasar ta yi wa Amirka bayan kafa sabuwar gwamnati.

https://p.dw.com/p/3rH8v
Weltspiegel | 26.03.2021 | Nord Korea | Tableau
Hoto: KCNA/REUTERS

A wani martaninta ga kalaman Shugaban Amirka Joe Biden a kan gwaje-gwajen manyan makamai, Koriya ta Arewa ta yi barazanar sake gwaje-gwajen nata, wani matakin murza gashin baki na farko da kasar ke yi tun bayan kafa sabuwar gwamnati a Amirka.

Koriya ta Arewar mai karfin makaman nukiliya, kasa ce da ta yi kaurin suna wajen nuna karfi ta wannan fuskar a duk lokacin da ta tasamma gabatar da wasu manufofi nata.

A ranar Alhamis da ta gabata ne dai kasar ta harba wasu makamai biyu daga gabashin gabar tekun Japan, abin kuma da Shugaba Joe Biden na Amirka ya ce ya saba wa yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya.

Hakan kuma ya biyo wani atisayin hadin gwiwa ne tsakanin sojojin Amirka ne da na Koriya ta Kudu, lokacin wata ziyarar da Sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken da na tsaro Lloyd Austin a yankin.