1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa ta mika wa Amirka gawarwakin sojojinta

Ramatu Garba Baba
July 27, 2018

A wannan Juma'ar, Koriya ta Arewa ta mika wa Amirka gawarwakin sojojinta 55 da suka mutu a yayin rikicin yakin da ya lakume rayukan miliyoyin jama'a.

https://p.dw.com/p/32Akn
USA Ankunft der toten US-Soldaten aus dem Niger
Hoto: picture alliance/AP Photo/L. Hiser/U.S. Army

Fadar White House ce ta tura wani jirgin sojojin kasar don kwaso wadannan gawarwakin bayan da Koriya ta cika alkawarin da ta dauka na mayar da gawarwakin a ganawar da shugaba Kim Jong Un ya yi da takwaransa Donald Trump a watan Yunin da ya gabata.

Shekaru fiye da goma Amirka ta kwashe ta neman a dawo mata da gawarwakin ba tare da samun nasara ba, a sakamakon sabanin da ke a tsakaninta da Koriya ta Arewa bisa shirin ta na nukiliya. An kiyasta cewa, sojojin Amirka dubu bakwai da dari bakwai ne suka bace a yayin yakin Koriya a tsakanin shekarar 1950-53.