1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Koriya ta Arewa ta yi gwajin makami

Ramatu Garba Baba
March 25, 2021

A wani abu mai kama da tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro, Koriya ta Arewa ta sake yin wani gwajin makami mai linzami da ke cin dogon zango a wannan Alhamis.

https://p.dw.com/p/3r5bV
Nordkorea: Raketenübungen unter Leitung von Führer Kim Jong Un
Hoto: picture-alliance/Yonhap

Masana na ganin, wannan ba sabon abu bane, don kuwa kasar ta saba irin wannan gwajin a duk lokacin da aka nada sabon shugaba a Amirka, a matsayin jan hankali, ko watakila, a koma kan teburin sulhunta rikicin nukiliyar da ya sa Amirkan lafta mata takunkumi. Ba a dai san martanin da gwamnatin Shugaba Joe Biden za ta mayar kan gwajin ba, gwajin da a duk lokacin da aka yi shi, ke haifar da fargaba a zukatan gwamnatocin kasashen duniya, kan shirin nukiliyar Koriya ta Arewa, da ake zargin na tattare da hadura. 

Amirka dai ta sanya wa Koriya ta Arewa takunkumi ne, bisa zarginta da tanadin kayan sarrafa makaman nukiliya, da gwajin sabbin makaman kare dangi da ta sake fasalta wa. Yunkurin sulhunta batun a tsakanin tsohuwar gwamnatin Donald Trump da Shugaba Kim Jong Un ya ci tura. Ana dai ci gaba da takaddama kan shirin nukiliyar Koriya ta Arewa da sauran manyan kasashen duniya.