1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa ta harba wani sabon makami

March 17, 2023

Koriya ta Arewa ta sake harba wani makami mai linzami da ke cin dogon zango, wanda ta ce ta yi shi ne da yammacin jiya Alhamis da nufin kada hantar makiya a cewarta.

https://p.dw.com/p/4Oot7
Hoto: KCNA/AP Photo/picture alliance

Koriya ta Arewar ta harba makamin ne a daidai lokacin da makwabciyarta Koriya ta Kudu da Japan ke amincewa da aiki kafada-da-kafada da Amurka ta fuskar tsaro a yankin.

Wannan ne dai karo na hudu cikin mako guda da Koriya ta Arewar ke cilla manyan makamai masu linzami da nufin murza gashin baki, a lokacin da kasashe makwabtan ta ke atisayen kaifafa basira da kuma dabarun yaki mai karfi cikin shekaru.

Kamfanin dillancin labaran Koriya ta Arewa, ya ce Shugaba Kim Jong Un ne ya sa ido a lokacin da aka harba makamin mai suna Kwason-17, yana mai jaddada bukatar razana wadanda ya kira abokan gaba, da suka hada da Amurka da Japan da ma Koriya ta Kudu.