1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa ta harba sabon makami

April 18, 2019

A karo na farko tun bayan tattaunawa tsakaninta da Amirka cikin watan Fabrairu, Koriya ta Arewa ta kera tare da gwada wani sabon makami.

https://p.dw.com/p/3H0Kj
Nordkorea Kim Jong Un besucht Flugtraining der Korean People's Army Air Force
Hoto: Reuters/KCNA

Kamar dai yadda kamfanin dillancin labaran kasar na KNCA ya ruwaito, makamin wani sabon samfuri ne na makaman yaki da ba a kira shi makami mai linzami ba.

Shugaba Kim Jong Un na Koriyar, ya shaida aikin gwajin da sojin kasar suka yi, inda ya ce hakan ya sake nuna irin karfin da kasar ke da shi ta fuskar yaki.

Ko cikin watan Nuwambar bara ma Shugaba Kim, ya kasance lokacin gwajin wani makamin da aka yi a kasar, gwaje-gwajen kuma da ke kada hantar Amirka matuka.