1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Koriya ta Arewa ta yi watsi da yunkurin sulhu da Amirka

July 27, 2021

Koriya ta Arewa ta sanar a wannan Alhamis cewa za ta yi watsi da tayin tattaunawa da Amirka ke mata har sai Amirkan ta janye manufofinta masu masu cutarwa.

https://p.dw.com/p/3qnIh
Nord Korea | Rede von Kim Jong Un
Hoto: Reuters/KCNA

Martanin na Koriya ta Arewan dai ya biyo bayan sanarwar da Amurka ta bayar ta bukatar kasashen biyu su tattauna a kan batun nukiliyar Koriya ta Arewa.

Babbar jami'a a ma'aikatar harkokin wajen Koriya ta Arewa Choe Son Hui ta ce tun da sabuwar gwamnati ta zo a Amirka, Koriyan ta Arewa ke ta jin soki-burutsu kala-kala da kuma yunkurin dakatar da ita daga mallakar makaman nukiliya, tana mai cewa irin wannan gayyata ta Amirka ba komai bace face wani salo ne na bata mata lokaci a kan harkokinta.

Koriya ta Arewan kuma ta yi amfani da wannan dama wurin mayar da martani ga atisayen sojin da koriya ta Kudu da Amirka suka yi a farkon watan nan, inda ta ce ikiriri Amirka ta nuna bangaranci ta shiga atisayen da aka yi da zummar cinta da yaki.